28 Disamba 2019 - 06:11
MDD Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Kan Jinkirin Amurka Na Ba da Visa Ga jami’an Diplomsiyar Rasha Da Wasu Kasashe .

Babban sakatare janar din Majalisar Dinkin duniya, Antonio Guterres ya bayyana cewa majalisar ta aike da sakon rashin jin dadinta game da yaddda Washington take bata lokaci kafin ta bada shedar Izinin shiga kasar wato VISA ga wasu jami’an diplomsiyar kasar Rasha da ma wasu kasashen duniya.

(ABNA24.com) Babban sakatare janar din Majalisar Dinkin duniya, Antonio Guterres ya bayyana cewa majalisar ta aike da sakon rashin jin dadinta game da yaddda Washington take bata lokaci kafin ta bada shedar Izinin shiga kasar wato VISA ga wasu jami’an diplomsiyar kasar Rasha da ma wasu kasashen duniya.

Wannan matakin ya zo ne bayan da kakakin MDD Stephen Dujarric ya yi karin bayani game da korafin da ma’aikatar haekokin wajen kasar Rasha ta yi na yin kunnen uwar shego game da bata lokaci da Amurka ta keyi wajen bada Visa,

A watan Satumba da ya gabata kimanin jami’an diplomasiyar kasar Rasha guda 10 ne Amurka ta hanasu Visa domin halartar taron babban zauren majalisar da aka gudanar, matakin da maktaimakin minstan harkokin wajen kasar rasha a bayyana shi da Isgili kuma ya sha alwashin mayar da martani mai zafi akai.

Rahotan da hukumar kula da hulda da Jama’a da mai masaukin baki ya fitar ya nuna cewa wakilin kasashen Iran Cuba Nicaragua Kotiya ta Arewa Rasha da kasar Siriya a majalisar dinkin duniya sun fadi cewa jami’an diplomasiyarsu da wasu ma’aikatansu na fuskantar matsaloli masu yawa da suka hada da bata lokaci da birninken kwakwab daga gwamnatin Amurka da ma hanasu Visa a wasu lokutan , da hakan karya yarjejeniyar da aka sanya hannun akai ne a lokacin sanya hedkwatar Majalisar ta kasance a Amurka a shekara ta 1947




/129